32.3 C
Abuja
Tuesday, January 25, 2022

Yajin aikin ƴan Adaidaita-sahu: Jami’ar Maitama Sule ta samar da motoci don jigilar ɗalibai

Must read

Yayin da a ka shiga rana ta biyu a yajin aikin da matuƙa baburan adaidaita-sahu su ka fara a Jihar Kano, Jami’ar Gwamnati ta Yusuf Maitama Sule Kano ta samar da motoci guda 7 domin jigilar ɗalibai don su samu su kammala jarrabawar da su ke yi.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a jiya ne dai matuƙa adaidaita-sahun su ka tsunduma yajin aikin domin nuna rashin goyon baya na kuɗaɗen haraji iri-iri da su ka ce gwamnatin jihar ta na takura musu su biya.
Yajin aikin ne ya sanya jami’ar ta dakatar da jarrabawar da ta ke yi a jiya Litinin.
Sai dai kuma a yau Talata, sai jami’ar ta sanar da samar da dogayen motoci domin jigilar ɗalibai.
A sanarwa mai ɗauke da sa hannun Shugaban Ɗalibai na jami’ar, Imam Muhammad Inuwa, wacce Daily Nigerian Hausa ta samu,  jami’ar ta zama jadawalin jigilar ɗaliban.
Sanarwar ta ce mota ta farko za ta yi jigilar ɗaliban da ga Mill Tara, Kwanar Ungogo, Bachirawa, Rijiyar Lemo, Kurna, Mahaɗar Dantata, Kofar Dawanau, Kofar Waika zuwa Main Campus.
Sannan kuma da ga ‘Main Campus’, motar, ƙirar kamfanin Tata za ta ɗauki Kabuga, titin BUK, Na’isa, Dan Agundi zuwa ‘City Campus’.
Mota ta 2 kuma za ta ɗauki ɗaliban jami’ar da ga Kwalejin Sa’adatu Rimi, Na’ibawa, Unguwa Uku, Gadar Lado, Asibitin Aminu Kano, Court Road, Zoo Road, Tukuntawa, Titin ultimate, Sharada Kwanar Kasuwa, Yahaya Gusau  Gadon Ƙaya Kabuga zuwa Main Campus.
Mota ta 3 kuwa za ta fara jigilar ta da ga Hotoro Mega Station, Titin Maiduguri , Gadar Lado, Dangi Round-about, Kano Line zuwa City Campus.
Haka-zalika mota ta 4 za ta fara da ga Tudun Wada gada, Gwagwarwa, Kisgadi, Bata, Triumph, Gwammaja, Kwanar Taya, Kofar Dawanau zuwa Main Campus.
Mota ta 5 za ta fara da ga BUK Newsite, Rijiyar Zaki, Jambulo, Kabuga zuwa Main Campus.
Mota ta 6 za ta taso da ga Asibitin Aminu Kano, Zoo Road, Dan Agundi, School of Hygiene zuwa City Campus.
Sai kuma mota ta 7 za ta yi jigila da ga Fanshekara, Zawaciki, Sabon Titin Dorayi, Karshen Waya, Kofar Famfo, FCE, Kansakali,Yan Rake, zuwa Main Campus da ga nan ta sace zuwa City Campus.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa sanarwar ta yi gargaɗin cewa sai wanda ya nuna katin shaidar zama ɗan makarantar ne a bari su shiga motocin, inda ta ƙara da cewa motocin za su fara jigilar ne da ga ƙarfe 9 na safe.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article