Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

AN shiga yakin cacar-baki tsakanin Shugaban majalisardattawa Bukola Saraki da Sanata Abdullahi Adamu tsohon Gwamnan jihar Nassarawa.

Ana musayar yawu ne tsakanin manyan Sanatocin biyu, sakamakon zargin da Abdullahi Adamu yayi na cewar Saraki na magana a bayan idon Dino Melaye, inda Saraki ya maida martani da cewar Abdullahi Adamu makaryaci ne.

Daga isani kuma Abdullahi Adamu yayi ikirarin cewar Sanata Bukola Saraki na yin zagon kasa ga Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Inda ya nemi Saraki da ya nemi afuwar Shugaba Buhari akan yadda ya dinga kwasar zunubbansa yayin da Buharin ke kwance a asibiti a kasar Burtaniya.