A wani abu da ake gani ba safai ba, da kuma yake kara nuna dankon alakarsiyasa tsakanin Kwankwasiyya da Mundubawa, ‘yan Kwankwasiyya da dama ne suke tururuwa zuwa Mundubawa gidan Malam Ibrahim Shekrau Sardaunan Kano, domin yin jaje ga Sardaunan kan abinda suke cewar Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa na yiwa Malamin bita da kulli.

A makon da ya gabata ne dai hukumar ta EFCC tayi awon gaba da tsohon Ministan Ilimi Malam Ibrahim SHekarau kan batun kudaden da suke da alaka da zaben 2015, hukumar ta gurfanar da Malam Shekarau tare da Amb AMinu Wali da kuma Injinya Mansur Ahmed a gaban kotun tarayya dake Kano.

Dubban magoya bayan malam Shekarau da jam’iyyar PDP ne suka yi tururuwa a harabar kotun domin nuna goyo baya ga jagoran nasu Malam Ibrahim Shekarau, inda har sai da ta kai ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masuzanga zanagar nuna goyon baya a harabar kotun.

Bayan da aka bayar da belin Malam Ibrahim Shekarau ne, mutane da dama suke ta yin tururuwa zuwa gidan Malamin dake Mundubawa domin jajanta masa wannan abu da ya same shi, cikinmasu zuwa wannan ziyarar jaje har da ‘yan Kwankwasiyya magoya bayan tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ake ganin suna rungumar juna da Malam Shekarau.