Tsohon Gwamnan kaduna, Ramalan Yero rike da allon masu laifi a hukumar EFCC

Mutane da yawa ne a shafukan sada zumunta na intanet suka ga baiken hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, kan yadda ta sanya hoton tsohon Gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero rike da wani allo da yake nuna shi mai laifi ne na cin kudade ba bisa ka’ida ba.

Mutane da dama ne suka caccaki hukumar ta EFCC akan abinda suka kira azarbabi da ta yi wajen kiran Ramalan Yero mai ‘laifi’ ba tare da kotu ta hukunta laifin da hukumar take zargin Ramalan Yero da aikatawa ba.

Har ya zuwa yanzu mutane na cigaba da caccakar hukumar EFCC kan batun inda da dama suka kira shi da tozartawa ga tsohon Gwamnan.