Hassan Y.A. Malik

Wata majiya ta cikin gida ta bayyana cewa ocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Gernot Rohr ya bayyana cewa zai yi amfani ne da jerin ‘yan wasan da ya yi amfani da su wajen doke tawagar Iceland a wasan da Super Eagles za ta kara da Ajantina a yammacin yau.

A yau din ma dai, Kelechi Iheanacho, Tyronne Ebuehi da Ahmad Musa za su fara, inda Odion Ighalo, Shehu Abdullahi da Alex Iwobi za su zo a benci.

Salon wasan da kocin zai buga shi ne na mutum 3 a baya, 5 a tsakiya, mutum 2 kuma a gaba a matsayin masu zura kwallo.

In ba a manta ba dai, da wannan salo ne Rohr ya yi mafani wajen doke Ajantina a wasan sada zumanta da aka tashi da ci 4 da 2.

A wasan na yau da za a take da karfe 7:00 na yama daidai, Super eagles na bukatar yin nasara akan Ajantina ko akalla ta yi canjaras da Ajantina don samun kaiwa ga zagaye na 16 na gasar cin kofin duniya

Ga jerin ‘yan wasa 11 da Nijeriya za ta fito da su:
Uzohu
Balogun
Ekong
Ebuehi
Idowu
Ndidi
Etebo
Mikel
Musa
Iheanacho
Moses