Home Labarai An yanke wa mutane 4 ɗaurin rai da rai bisa yi wa ƴar shekara 14 fyaɗe a Jigawa

An yanke wa mutane 4 ɗaurin rai da rai bisa yi wa ƴar shekara 14 fyaɗe a Jigawa

0
An yanke wa mutane 4 ɗaurin rai da rai bisa yi wa ƴar shekara 14 fyaɗe a Jigawa

Wata babbar kotu a jihar Jigawa ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu mutane hudu da suka yi wa wata yarinya ƴar shekara 14 fyade a unguwar Kurmi da ke karamar hukumar Gwaram a jihar.

Daily Trust ta rawito cewa wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Sale Ibrahim, mai shekaru 40, Amadu Saleh, shekaru 46, Sale Ali, shekaru 40 da Danmami Yusuf, mai shekaru 37.

Lauyan mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu hudu da suka hada da rahoton likita tare da gabatar da wasu hujjoji guda biyu don tabbatar da kararsa.

Bayan sauraron dukkan bangarorin biyu a shari’ar, kotun ta ce lauyan mai gabatar da kara ya tabbatar da zargin sa ba tare da wata shakka ba.

Don haka kotun ta samu wadanda ake tuhuma da laifin fyade wanda ya sabawa sashe na 3 (1) da kuma hukuncin da ya dace a karkashin sashe na 3 (2a & 2b) na dokokin cin zarafi na VAPP na jihar Jigawa da ake tuhumarsa.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne babbar kotun jihar ta yankewa wani mutum Aminu Ali mai + 25 hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifin aikata fyade da luwadi.