
Bayan wata ɗaya a hannun masu garkuwa da mutane, masu bauta a cocin emanuel baftis da ke Kakau Daji, Jihar Kaduna sun shaƙi iskar ƴanci.
A ranar 31 ga watan Oktoba ne dai masu ibadar su na tsaka da bauta a cikin cocin, sai ƴan yadda su ka dirar musu, inda su ka yi awon-gaba da mutum 60 da ga cikin su.
Bayan ƴan kwanaki, sai ƴan ta’addan su ka hallaka uku da ga ciki sannan su ka kaiwa biyu munanan raunuka bayan sun nemi a basu kuɗin fansa.
Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasar, reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab ne ya baiyana sakin masu bautar a yau Asabar.
Ya ƙara da cewa a kwai wasu mutane 9 ma da a ka sake su tare da ƴan cocin a jiya Juma’a da daddare.
Sai dai kuma Hayab bai baiyana cewa ko sai da a ka biya kuɗin fansa sannan a ka saki masu bautar ba, ya ce dai kawai ma’aikatan cocin ne su ka sanar da shi sannan sojoji sun tafi da su bariki.