Home Labarai YANZU-YANZU: APC ta dakatar da Ganduje kan zargin cin-hanci da rashawa

YANZU-YANZU: APC ta dakatar da Ganduje kan zargin cin-hanci da rashawa

0
YANZU-YANZU: APC ta dakatar da Ganduje kan zargin cin-hanci da rashawa

Jam’iyyar APC, reshen mazabar Ganduje a Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano, ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a karamar hukumar, Halliru Gwanjo ne, ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a yau Litinin.

Gwanjo, ya ce sun yanke shawarar dakatar da Ganduje, tsohon gwamnan Kano, daga jam’iyyar ne, sakamakon zarge-zargen da gwamnatin Jihar Kano ke masa kan cin hanci da rashawa.

Sanarwar ta ce dakatarwar ta fara aikin ne daga yau Litinin 15 ga watan Afrilu, 2024 har zuwa lokacin da aka kammala shari’ar Ganduje din.

Tuni dai gwamnatin Kano ta maka Ganduje a kotu, inda ake sa ran gurfanar da shi a ranar 17 ga watan Afrilu.

Sai dai kuma da aka tuntube shi, shugaban APC na jiha, Abdullahi Abbas ya ce tuni jam’iyyar ta dauki matakin dakatar da waɗanda su ka ce sun dakatar da Ganduje din.

A cewar Abbas, tuni aka dakatar da su na tsawon wata 6 kuma an kafa kwamitin bincike don gano zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa da ake musu.

Abbas ya kara da cewa an samu kwararan hujjoji na yi wa jam’iyya zagon-ƙasa a kan su, musamman ma ganawar sirri da aka kama su sun yi da jami’an gwamnati mai ci.