Home Labarai YANZU-YANZU: Atiku ya jajanta wa Tinubu bayan ya faɗi a wajen bikin ranar dimokraɗiyya

YANZU-YANZU: Atiku ya jajanta wa Tinubu bayan ya faɗi a wajen bikin ranar dimokraɗiyya

0
YANZU-YANZU: Atiku ya jajanta wa Tinubu bayan ya faɗi a wajen bikin ranar dimokraɗiyya

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya jajanta wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa faduwa da ya yi yayin hawa mota a wajen taron bikin ranar dimokraɗiyya ta bana.

Wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan kafofin sadarwa ya nuna Tinubu, ya ci tuntuɓe yayin da ya hau mota domin duba faretin bikin ranar dimokraɗiyya ta bana.

Bayan ya ci tuntuɓen ne kuma sai ya faɗi a cikin motar, wacce ta ke buɗaɗɗiya, lamarin da ya sanya dogaransa su ka yi maza su ka ɗago shi.

Bayan an ɗago shi kuma sai Tinubu, wanda ba a ga wata alamar jikkata a jikinsa ba, ya ci gaba da duba faretin.

A sakon nasa da ya wallafa, a shafinsa na X, Atiku ya jajanta wa Tinubu, inda ya kuma yi masa fatan lafiya da kuma fatan bai ji rauni ba.

“Ina jajanta wa Shugaba Bola Tinubu a bisa abinda ya faru a wajen faretin bikin ranar dimokraɗiyya. Ina fatan dai babu wata matsala,” in ji Atiku.