Home Labarai YANZU-YANZU: Gwamnan jihar Ondo, Akeredelu ya mutu

YANZU-YANZU: Gwamnan jihar Ondo, Akeredelu ya mutu

0
YANZU-YANZU: Gwamnan jihar Ondo, Akeredelu ya mutu

Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, wanda ya sha fama da jinya, ya mutu. Ya mutu yana da shekara 67 a duniya.

Iyalinsa da wasu manyan jami’an gwamnati ne su ka tabbatar da mutuwar ta sa a yau Laraba.

Gwamnan ya mutu ne bayan doguwar rashin lafiya da ba a san ko wacce iri ba ce, amma dai ana raɗe-raɗin ko cutar konewar jini (leukemia) ce sanadin mutuwar ta sa.

A ranar 13 ga watan Disamba ne gwamnan ya danƙa ragamar mulki ga mataimakin sa, Lucky Aiyedatiwa domin tafiya neman lafiya a Germany.

Kafin nan ma ya dade a kasar waje domin neman lafiya.

Marigayin ya mutu ya bar matar sa, Betty, da ƴaƴa huɗu.