
Gwamnatin tarayya ta ce da ga 1 ga watan Oktoba za ta fara siyar da danyen mai ga matatar man Dangote da Naira ba da Dalar Amurka ba.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa ma’aikatar kudi, a wata sanarwa da ta fitar a yau Litinin ta ce an dau matakin ne a ganawar kwamitin aiwatar da tsarin karkashin jagorancin Wale Edun, ministan kudi.
Hakan dai na zuwa ne bayan umarnin shugaban ƙasa Bola Tinubu na siyarwa da Dangote ɗanyen mai da kuɗin Naira.
A watan Agusta da muke ciki ne ake sa ran matatar man ta Dangote zata fara fitar da man fetur tatacce.