
Gwamnonin APC sun miƙa sunayen ƴan takarar shugabancin ƙasa guda biyar ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari domin ya zabo wanda ya amince da shi.
Daily Trust ta rawaito cewa wata majiya ta ce sunayen sun haɗa da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, gwamna Kayode Fayemi (jihar Ekiti), Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, da kuma gwamna Dave Umahi ( Jihar Ebonyi).
Gwamnonin, bayan ganawar da suka yi da shugaban kasar sun ce za su koma Villa bayan sun gana da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) da sauran masu ruwa da tsaki.