
Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku saboda zargin da ya yi na cewa an yi cushen naira tiriliyan 3.7 a kasafin kudi na 2024 a wata hira da BBC Hausa.
A yayin hirar, Ningi ya ce kungiyar Sanatocin Arewa za ta fito da batun ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Shugaba Bola Tinubu, inda ya kafe cewa an zartar da wani kasafin kudin “ta karkashin kasa.”
A zaman majalisar na yau Talata, Sanata Adeola Solomon (Ogun ta yamma) ya gabatar da kudiri ga Sanatocin da su yi muhawara kan wannan zargi, inda ya ce hakan ya saba wa damarsa a matsayinsa na Sanata wanda ke cikin wadanda suka amince da kasafin kudin a zauren majalisar.
Sanata Ned (Edo ta Kudu) ne ya goyi bayan kudirin nasa.
Bayan doguwar muhawara da Sanatoci suka yi kan lamarin, Sanata Jimoh Ibrahim (APC Ondo ta Kudu), ya ce a dakatar da Ningi na watanni hudu.
Shi ma da yake bayar da gudunmawa, Sanata Asuquo Ekpenyong (Cross River ta Kudu) ya roki a ƙara wa’adin zuwa watanni 6.
Sai dai Sanata Sani Musa (APC Niger) ya ba da shawarar a dakatar da Ningi na tsawon watanni 3 sannan kuma a sanya shi ya rubuta takardar neman gafara ga majalisar dattawa.
Bayan tafka muhawara, Akpabio ya ce, “An dakatar da Sanata Ningi na tsawon watanni 3 kuma an cire shi daga dukkan ayyukan majalisar na tsawon watanni uku.