Home Labarai YANZU-YANZU: NNPC ya ƙaryata rahoton ƙarin farashin man fetur

YANZU-YANZU: NNPC ya ƙaryata rahoton ƙarin farashin man fetur

0
YANZU-YANZU: NNPC ya ƙaryata rahoton ƙarin farashin man fetur

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa babu wani shiri na karin farashin man fetur.

Tun a farkon makon nan ne aka fara yada jita-jita cewa NNPC na shirin kara farashin man fetur zuwa Naira 1,200 kan kowace lita.

Sai dai kuma a wani martani da ya mayar, kamfanin mai na Najeriya ya karyata jita-jitar, inda ya bayyana hakan a matsayin zance mara tushe, kamar yadda Olufemi O. Soneye, babban jami’in hulda da jama’a na kamfanin NNPC Ltd ya bayyana a Abuja a yau Laraba.

“Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC, Ltd yana tabbatar wa jama’a cewa babu wani shiri na karin farashin man fetur.

“NNPC Ltd. ya bukaci ƴan Najeriya da su yi watsi da jita-jitar da ba su da tushe balle makama, kuma ya ba su tabbacin cewa babu wani shiri na sake kara farashin man fetur.

“Sabo da haka mu na shawartar masu ababen hawa a duk fadin kasar da kada su yi rigegeniyar sayen man fetur saboda a halin yanzu akwai wadatar man a duk fadin kasar,” in ji takaitacciyar sanarwar.