An sako wasu ƙarin mutane uku da aka yi garkuwa da su a harin da aka kai kan jirgin kasa a watan Maris daga hannun ƴan ta’adda.
An sako fasinjojin, wadanda ke cikin mutane da dama da aka yi garkuwa da su a ranar 28 ga Maris.
Tukur Mamu, mai taimakawa Ahmad Gumi, malamin addinin Islama, wanda ya tsunduma cikin tattaunawar neman sakin mutanen, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Wannan ci gaban ya zo ne sa’o’i bayan da a ka fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda ƴan ta’addan ke zane wadanda aka yi garkuwa da su da bulala.