Home Labarai YANZU-YANZU: Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kudin 2024 na Naira tiriliyan 28.78

YANZU-YANZU: Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kudin 2024 na Naira tiriliyan 28.78

0
YANZU-YANZU: Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kudin 2024 na Naira tiriliyan 28.78

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 na Naira tiriliyan 28.78 a matsayin doka a fadar shugaban kasa da ke Abuja a yau Litinin.

Shugaba Tinubu, wanda ya dawo fadar Aso Rock Villa awa daya da ta gabata daga hutun Kirsimeti da ya yi a Legas, ya gudanar da wani takaitaccen biki na rattaba hannun ko kan kasafin kudin kaddamar da gwamnatinsa.

Taron dai ya samu halartar manyan jami’an gwamnati.

A karshen makon da ya gabata ne dai majalisar dokokin kasar ta zartar da kudurin kasafin kudin shekarar 2024, inda ta kara girmanta daga kudirin da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar na Naira Tiriliyan 27.5 da aka yi tun farko zuwa Naira Tiriliyan 28.7. Girman kasafin kudin ya samu karin Naira tiriliyan 1.2.