Home Labarai YANZU-YANZU:Tinubu ya ba da umarnin sake bude bodar Nijeriya da Nijar

YANZU-YANZU:Tinubu ya ba da umarnin sake bude bodar Nijeriya da Nijar

0
YANZU-YANZU:Tinubu ya ba da umarnin sake bude bodar Nijeriya da Nijar

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin bude iyakokin Najeriya ta kasa da ta sama da Jamhuriyar Nijar tare da dage wasu takunkumai da aka ƙaƙaba wa ƙasar.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a yau Laraba, ta ce wannan umarnin ya yi daidai da shawarar da kungiyar ECOWAS ta yanke a babban taronta na musamman da ta yi a ranar 24 ga Fabrairu, 2024, a Abuja.

Shugabannin ECOWAS sun amince da dage takunkumin karya tattalin arziki da suka kakabawa Jamhuriyar Nijar, Mali, Burkina Faso, da Guinea.

Shugaban ya bayar da umarnin a dage takunkumin da aka kakaba wa Jamhuriyar Nijar nan take: