Home Labarai YANZU-YANZU: Tinubu zai katse tafiyarsa zuwa Faransa don rantsar da sabuwar CJN a Nijeriya

YANZU-YANZU: Tinubu zai katse tafiyarsa zuwa Faransa don rantsar da sabuwar CJN a Nijeriya

0
YANZU-YANZU: Tinubu zai katse tafiyarsa zuwa Faransa don rantsar da sabuwar CJN a Nijeriya

Ana tsammanin shugaban kasa Bola Tinubu zai dawo Nijeriya a gobe Juma’a don rantsar da Kudirar Kekere-Ekun a matsayin sabuwar Babbar Mai shari’a ta Nijeriya, CJN.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, shugaban kasar zai hau jirgi don dawowa Nijeriya a daren yau Alhamis.

Za a yi bikin rantsar da sabuwar babbar mai shari’ar ne a fadar shugaban kasa.

A ranar Litinin ne dai Tinubu ya tafi kasar Faransa domin hutawa.

A yau Alhamis kuma, Olukayode Ariwoola ya kammala aikinsa a matsayin babban mai shari’a na Nijeriya.

Majalisar shari’a ta kasa NJC, ta bada shawarar nada Kekere-ukun a matsayin babban mai shari’a.