23.1 C
Abuja
Tuesday, February 7, 2023

YANZU-YANZU: Ƙungiyar masu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ta dakatar da Ciyaman ɗin Kano Pillars

Must read

 

Ƙungiyar Masu Ƙungiyoyin Ƙwallon ƙafa ta Ƙasa ta dakatar da shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Yahaya Surajo har sai baba-ta-gani, saboda halin da ya nuna a lokacin wasan mako na 31 da ƙungiyar ta kara da Dakkada FC a Kano a jiya Alhamis.

A cikin wani faifan bidiyo ne, a ka ga Surajo ya kai wa wani mataimakin alkalin wasa naushi a wasan, lamarin da kungiyar ta bayyana a matsayin abin takaici, wanda ba za ta amince da shi ba kuma hali da zai iya bata mata suna.

“Don haka ƙungiyar masu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa din ta dakatar da shugaban kungiyar ta Kano Pillars, Malam Yahaya Surajo daga dukkan ayyukan kungiyar har zuwa lokacin da za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin,” Alloy Chukwuemeka, Sakataren zartarwa na kungiyar. , in ji sanarwar.

Ƙungiya ce da ts hada da hazikan masu kula da kwallon kafa wadanda suka yi fice a fagage da dama na fannin rayuwa da ake sa ran za su ba da horo sosai wajen gudanar da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daban-daban.

Kungiyar ta fusata kan halin Surajo wanda ya zo kasa da sa’o’i 48 bayan wani taron hadin gwiwa da LMC, inda ta yi gargadi game da ayyukan da za su iya haifar da mummunan zato ga gasar.

Shugaban kungiyar Barr. Isaac Danladi, ya ce ciyaman ɗin na Kano Pillars zai fuskanci kwamitin ladabtarwa don kare kansa kafin a sake shigar da shi cikin kungiyar.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article

- Website Designed By DEBORIAN.COM, a Nigerian Web Designer and Web Developer -