
A yau ne man fetur da matatar mai ta Dangote ta fara fitarwa zai shiga kasuwa a Nijeriya kamay yadda Nairametrics ta tabbatar.
Matatar wacce ke iya tace gangana dubu 650, 000 a rana guda, ta samu nasarar kammala gwajin fitar da man kuma ta shirya bayar da shi don siyarwa.
Ana tsammanin matakin zai saukaka matsalar karancin mai a fadin kasar nan.
Wasu majiyoyi sun ce kamfanin mai na kasa NNPC, ne zai kasance wanda zai dinga siyan man daga matatar mai ta Dangote wacce ke birnin Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa, Aliko Dangote, shugaban matatar zai kasance a matatar domin shaida yadda za a fara siyar da man a karon farko.
Nairametrics