Daga Hassan Y.A. Malik

An haifi Malam Aminu Kano a shekarar 1920 a cikin birnin Kano.

Marigayi malam Aminu kano ya yi karatun Al-Qur’ani mai tsarki a wajen shehun malami, Malam Halilu. Malam Halilu shi ne limamin sarkin Kano ABDULLAHI BAYERO a shekarar 1929 zuwa 1953.

An sa malam Aminu kano a makarantar primary ta SHAHUCI da ke Kano a shekarar 1930 lokacin yana dan shekara goma da haihuwa.

Ya zama dalibin kwalejin kaduna wadda aka samar da ita a 1922 da sunan kwalejin Katsina a Katsina daga 1937 zuwa 1942.

Bayan ya gama kwalejin Kaduna ne, Malam Aminu Kano ya samu aikin koyarwa a makarantar Middle School da ke Bauchi, inda a lokacin Sir Abubakar Tafawa Balewa ya ke a matsayin Headmaster.

Daga Bauchi Middle School sai aka canzawa Malam Aminu Kano wajen aiki zuwa kwalejin horar da malamai ta Maru da ke gundumar Sokoto a matsayin headmaster a shekarar 1949 inda ya yi shekara daya a nan kafin daga nan ya ajiye harkar aiki ya kama harkokin siyasa gadan-gadan.

Malam Aminu Kano ya fara sansanar harkokin siyasa ne tun a shekarar 1943 lokacin da ya taimakawa malam Sa’adu Zungur suka kafa wata kungiyar siyasa mai suna kungiyar cigaban Bauchi a jihar Bauchi a shekarar 1946.

Malam Aminu Kano da Malam Sa’adu Zungur sune suka karfafa kafuwar jam’iyar NEPA wato NOUTHERN ELEMENT PROGRESSIVE ASSOCIATION kafin daga baya takoma NEPU wato NOUTHERN ELEMENT PROGRESSIVE UNION, an kafa jam’iyar ne a shekarar 8 ga watan 8 a shekarar 1950 kuma da mutane 8 aka kafa jam’iyar.

A shekarar 1947 ne Malam Aminu Kano ya jagoranci bude wata kungiya ta malaman arewacin Nigeria, kuma da shi aka bude jam’iyar mutanen arewa wadda daga baya ta rikede ta koma LPC a shekarar 1949 a matsayin jam’iyar da ke taimakawa mutanen arewa.

Malam Aminu Kano ya rungumi harkokin siyasa sosai wanda har hakan tasa ya ajiye aikinsa a ranar 4 ga watan Nuwamba a shekara 1950.

Malam Aminu Kano ya zama shugaban jam’iyar NEPU ta kasa a shekarar 1953 har zuwa lokacin da aka yi juyin mulki na farko a Nigeria.

Ya taba cin zabe inda ya zama dan majalisar tarayya a shekarar 1959 zuwa 1966 inda ya wakilci Kano ta gabas a karkashin jam’iyar NEPU, shine me tsawatarwa a majalisar hadin gwiwar, kuma ya rike kwamishan lafiya na tarayya kuma dan majalisar zartarwa na koli a gwamnatin tarayya a lokacin mulkin Yakubu Gowon.

Malam Aminu Kano da shi aka yi ta gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga hannun farar hula a zamanin Yakubu Gowon wanda Yakubun ya daga bayar da mulkin wanda a dalilin hakan ya haddasa hanbarar da gwamnatin Gowon din a shekarar 1975 inda Murtala Muhammed ya gajeshi.

Da shi aka yi gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga farar hula a shekarar 1979.

Malam Aminu Kano shine shugaban jam’iyar PRP kuma dan takararta na shugabancin kasa a shekarar 1979.

Allah ya dauki ran Malam Aminu Kano a ranar Asabar 17 ga watan Afrilu, a shekarar 1983, a tsawon shekarunsa na 63 ya shafe shekaru 40 yana gwagwarmayar siyasa dan talakan arewa.

Ya yi kaurin suna wajen kin manufofin turawa dama duk wanda zai kawowa arewa wargi, mutum ne wanda bashi da kwadayi kuma baya siyasar kudi face akida zalla kawai.

Indai ka jiyo shi to akan arewane, duk kungiyoyin da ya yi ko ya jagoranta to gaba dayansu za kuji na AREWA ne.

Bayan mutuwar marigayi Malam Aminu Kano an sawa muhimman wurare sunansa kamar irinsu filin jirgin sama na Kano wato Malam Aminu Kano Airport da kuma asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano wato Aminu kano Teaching Hospital.

Allah ya jikan Malam Aminu Kano! Ya Allah kasa matasan arewa su yi koyi da irin halayyar wadannan bayin Allah nagari, wanda komai nasu akan arewa ne, basu da wayo sai sunji za’a illata AREWA!