Yusuf Buhari

Dukkan yunƙurin da aka yi domin mayar da Yusuf Buhari zuwa sashin masu fama da matsalar ƙwaƙwalwa na babban asibitin ƙasa dake birnin tarayya Abuja yaci tura daga asibitin Cedarcrest. Duk kuwa da cewar daman can mutane sun sha fadin cewar, iyalan Shugaban kasa basu gamsu da asibitocin Najeriya ba.

A ranar Laraba, jaridar DAILY NIGERIAN ta fara bayyana halin da Yusuf Buhari yake ciki sakamakon mummunan hadarin babur din da yayi, wanda Yusuf Buhari tare da abokin tserensa Bashir Gwandu suka yi taho mu gama abinda ya jefa su cikin wani mummunan hali.

A daidai lokacin da aka fara tunanin mayar da Yusuf Buhari zuwa babban asibitin kasa dake Abuja domin cigaba da jinyarsa acan, Gwamnatin tarayya ta sa aka fara yiwa sashin masu fama da matsalar kwakwalwa dake asibitin kwaskwarima domin samarwa dan shugaban kasar yanayi mai kyau.

“Ko ina a sashin da ake zaton za’a kai Yusuf Buhari anyi masa kwaskwarima, anyi fenti a ko ina, amma duk da haka sai aka zabi a bar Yusuf Buhari ya cigaba da jinya a sashin masu mummunar karaya, maimakon sashin masu fama da matsalar kwakwalwa inda wannan ita ce matsalar da Yusuf Buhari yake fama da ita a yanzu” A cewar wani makusanci ga iyalan Shugaban kasa.

Haka kuma, inda ake sa ran za’a kai Yusuf Buhari a babban asibitin kasa dake Abuja, sai da Ministan lafiya na tarayya ya kai ziyara asibitin domin duba sashin da za’a kwantar da dan gidan Shugaban kasar.

Wadan da suka ce da zarar Yusuf Buhari ya farfado a dauke shi zuwa kasar waje sune suka janyo aka fasa mayar da shi babban asibitin kasa dake Abuja. Ana sa ran daga zarar halin da Yusuf Buhari ya kyautata za’a fitar da shi zuwa kasar waje domin yin jinyarsa a can.

Wasu bayanai sun tabbatar da cewar, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kalubalanci jami’an tsaro akan dan me zasu kyale dansa Yusuf ya tuka wannan babur mai tsananin gudu.