Na Ahmed Ibrahim

Babu shakka, Shugaba Buhari ba ya wakiltar abin da muke buqata a yau da kuma gobe. A yau Nijeriya tana cikin wani hali na rashin xorewar tarihi da kuma kasa koyon darasi daga abin da ya faru baya. Ba za a taba samun waraka daga kansar da Nijeriya take fama da it aba har sai ta sami kulawa daga kwararrren likita wanda abin takaici, a yanzu ba mu da shi. Wadanda ba za su iya tuna jiya ba za su maimaita kuskurensu, kamar yadda aka saba cewa. Shugaba Buhari ba ya kiyaye tarihi wannan shi ya haifar da raggon salon shugabancinsa wanda ya haifar da dorarriyar rashin kulawa da fahimtar muhimmancin yadda ‘yan kasa ke ji game da yadda ake jagorantar su. Ya ake kallon halin ko-in-kula na wannan gwamnati wajen kimtsa da tsara da lura da saisaita dadaddiyar bangaranci da ninanci da kabilanci? Tir da irin wannan rikon sakainar kashi ga al’umma. Lura da irin tarihin Nijeriya da tsarinta da muradunta mabambanta wadanda a wata fuskar suke da hadari ga junansu, zai fi kyau a ce jagorantar Nijeriya ya fi karfin shugaban da ba shi da tsarin tafiya da kowa da kowa da mabambanta tsare-tsare cikin sha’anin jagoranci.

Babu shakka zaben shekarar 2015 ya kasance marabar da ta rarraba kan ‘yan Nijeriya a tsawon tsarin dimukuradiya. Nijeriya ta kasance gab da rushewa. Duk da haka, hadin kan kasar ya dore. An yi zaton janaral din bayan ya karbi gadon yankunan da suke gab da rarrabuwa, zai samar da tsarin da zai hade kan bangarorin ya kuma fahimci dalilai na mu’amala da suke tunzura kowane bangare da kuma korafe-korafensu. Amma kash! Hakan ba ta kasance ba. Maimakon haka, sai muka sami murdadden shugaba mai nuna kabilanci, wanda tun a farkon mulkinsa bai bada lokacinsa baya kuma nuna rashin damuwarsa karara inda har ya ce “wadanda basu zabe shi ba ko kuma kaso uku cikin dari (3%) ne kawai suka zave shi ba za su taba samun romon mulkinsa kamar wadanda kaso tamanin da bakwai 97% suka zabe shi ba.” A cewarsa, “adalci shi ne” gwamnati ta yaba ga wadanda suka taimaka wajen kafa ta. Tir da wannan furuci!

A halin da ake ciki, Nijeriya tana bukatar wanda zai harhada kan bangarorin da suke gab da rarrabuwa wanda salon da wannan gwamnati ta dauka ya haifar. Nijeriya tana bukatar shugaban da zai hada kan dukkan shiyyoyinta ya kuma ba mabambantan kabilunta kwarin gwiwa ta yadda za a rika kula da bukatunsu a kuma kare su. Ba zai yiwu mu cigaba da zama da shugaban da bai ma kula da kansa ba, mai karancin fahimta, mai tsukakken tunani da salo. Idan har a matsayinsa na dan shekaru 76 da kuma kasancewarsa tsohon soja da ya kai matakin janar, ba zai iya samun amintattun ma’abota daga kowane bangare ba, kenan bai dace da shugabantar kasa mai sarkakiya da yawan al’umma kamar Nijeriya ba.

Za a iya kawar da irin rashin jituwa da rashin aminci da zargin juna da ke tsakanin ‘yan Nijeriya ne kawai idan an sami shugaban da ya san abin da yake yi, mai hangen nesa kuma dan kishin kasa wanda ya yi wani hobbasa na warkar da ciwon rashin da’a da kin aminta da kananan kabilu a matsayinsu na ‘yan kasa da suke da ruwa-da-tsaki wajen sha’anin jagorancinsu da gwamnatin APC ta haifar. Ba mu gode wa gwamnatin APC ba da ta fadada gibinmu ta kuma sake rarraba kanmu ta fuskar kabila da yanki da kuma addini ta yadda ta tsara mukaman tsaro wanda kabila daya ta mamaye. Shata iyakar kasa da taken kasa ba shi ke tabbatar da kasa ba. Batun ya wuce milyoyin eka na fadin kasa da takaitattun dangayen waka! Abin da yake tabbatar da kasa shi ne yarda da juna da marabtar juna da amincin da dan qasa ke da shi ga kasarsa. Duniyarka ta kusa karewa idan ba ka da ta cewa a gidan da ka gina. A yau, dan kabilar Ibibio a yankinsa ba lallai ne ya damu da Nijeriya saboda dalilinsa cewa ba shi da wanda zai kare muradunsa, kuma mutanen da ya kamata su kare muradun nasa ba su yi wani yunkuri na tabbatar masa da cewa ana kare muradun nasa. Me ya fi wannan takaici?!

Zan so in gutsiro wani abu daga kalamin Chris Ngwodo da yake cewa: tarihi yana koya babban darasi a yanayin gazawa. Da gaske ne ba a rana guda aka gina qasar Rome ba. Kuma ba a rana guda ta rushe ba. Rushewar wannan babbar daula ya faru ne cikin tsawon fiye da karni biyu da mamulkanta suka shafe suna suna siyasar bauta wa kai da abin da daular baya suka yi na rarrabuwa da ta kai ga rushewar daular. A Nijeriya, hadarin shi ne rashin tabukawar gwamnati na tsawon lokaci shi ne dalilin da zai iya kai mu ga rushewa.

Nijeriya tana bukatar fiye da abin da APC take ba mu. Cikin duk ‘yan takaran da muke da su, mutumin da mutumtakarsa da siffarsa da asalinsa suka nuna yana da alamun tafiya da kowa da kowa, kuma yake da tasiri da amsuwa ga kowa shi ne Alhaji Atiku Abubakar. Atiku shi ne mutumin da Nijeriya ke bukata yanzu, wanda zai hada kai da daidaita al’umma.  Yanayinsa da kuma amsar da aka yi masa a matsayin “dan halak” ya sa ya zama mafi dacewar dan takara da zai iya zama a gida yana kallon Bikin Al’ada na Abiriba; ba zai damu da sauraron wakokin Jukun na Ukenho ba; kuma zai yi rawar kidan Bikin Egungun.

Tarihin Atiku a matsayin kwararren maharbi ya sa ya kasance dan takarar da zai iya kutsawa tsawon zango daga inda yake zaune domin nema da lalubo mutanen da zai yi aiki da su wadanda za su iya yin abin da ya kamata ba tare da wani tsukakken tunani ba. Kasancewarsa kwararren dan kasuwa wanda ya yi nasara wajen gudanar da kasuwancinsa kuma ya san cewa kwazo da gaskiya da hazaka da sadaukarwa da sauransu suna da muhimmanci a makamar kowane rukuni ya tabbatar da fadin “zai nada mutanen da ya sani ne kawai”, za a iya cewa ya cancanta da aikin. Ya san cewa irin wadannan  dabi’u ko halaye an rarraba su cikin kowanne yanki tun asali.  Wannan shi ne irin shugaban da Nijeriya take bukata, wannan shi ne irin shugabancin da Alhaji Atiku Abubakar zai samar.

Ahmed Ibrahim ya rubuta daga Abuja