Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna,Malam Nasiru El-Rufai a ranar laraba ya gana da Shugabannin kungiyoyin Fulani a yankunan masarautun jihar 32 domin tattauna hanyoyin samar  da dawwamammen zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya bukace su da su yi duk abinda ya dace domin samar da zaman lafiya a dukkan fadin jihar, sannan kuma su tabbatar yaransu suna zuwa makaranta domin samun ilimi mai inganci.

“Mun kirawo wannan taron ne domin tattauna batun zaman lafiyar jihar Kaduna. Zaman lafiya shi ne abinda muka fi bukata yanzu”

“Zamu tsaya kai da fata wajen yin aiki da dukkan jami’an tsaro domin tabbatar da samun zaman lafiyar jihar Kaduna”

“Dole ne kowa ya kiyaye yin dukkan wani abu da zai kawo yamutsi da rashin zaman lafiya”

“Samun ingantaccen ilimi shi ne ginshikin samar da zaman lafiya mai dorewa. Duk al’ummar da ba ta da ilimi to ta gama lalacewa”

“Sai da ilimi ne zamu iya koyar da al’ummarmu domin kaucewa maganganun da zasu tayar da hayaniya, sannan su kaucewa rikici ko wanne iri ne, sannan kuma a kaucewa duk wani abu da yake da alaka da talauci da rashin aikin yi, idan babu ilimi duk wannan ba zai yuwu ba” A cewar Gwamnan jihar Kaduna.