Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban najeriya, Muhammadu Buhari yayi kiran da a kwantar da hankali a kasar Zambabwe, sannan kuma, yayi kira da a mutunta kundin tsarin mulkin kasar Zambabwe, sakamakon wani abu da ake ganin juyin Mulki ne aka yi shugaban kasar Robert Mugabe.

Shugaban ya bayyana hakan ne, a wata sanarwa ta musamman da mai taimaka masa na musamman akan kafafen yada labarai Femi Adesina, ya fitar a birnin Abuja a ranar laraba.

Shugaba Buhari ya bukaci shugabannin siyasar kasar da jami’an tsaron soja da su guji dukkan wani yunkuri da zai kai ga zubarda martabar kasar da kuma wani abu da zai kai ga zubar da jinin al’ummarsu, abin da ka iya zubar da mutuncin nahiyar Afurka baaki daya.

Ya bayyana cewar, ya kamata ayi dukkan mai yuwuwa wajen dawo daal’amura yadda suke, ta hanyar bin tanade tanaden kundin tsarin mulkin kasar, domin kare kasar daga aukawa zuwa wani hautsinin siyasa, wanda ba zai haifarwa da kasar da mai ido ba.

Wannan kira na Shugaba buhari ya zo ne, bayan da aka bayar da labarin cewar sojoji sun karbe ikon kasar, sakamakon turka turkar siyasa ta ta hargitse a kasar dake yankin kudancin nahiyar Afurka.

A nasa bangaren, Shugaban kasar Afurka ta kudu, Jecob Zuma, yace, duk da cewar Mugabe na tsare a kasarsa, amma muna da labarin halin da yake ciki mai kyau ne, babu wani mugun labari dangane da lafiyarsa.

Jecob Zuma, yace yayi magana da Robert Mugabe ta wayar tarho a matsayinsa na shugaban cigaban kasashen yankin kasashen kudancin nahiyar Afurka. Ya bayyana cewar, tuni ya tura wata tawaga zuwa Harare domin ganawa da mugabe da kuma manyan jami’an tsaron kasar da suka karbe iko a kasar.

Jami’an tsaron soji sun karbe ikon wani sashen kasar ne,kwanaki biyu bayan shugaban hafsan sojan kasar, janar Constantino Chiwenga, wanda ke tsaye cikin manyan jami’an tsaron kasar, yana bayyana cewar, a shirye yake yamutsin da ya barke a jam’iyya mai mulki Zanu-PF.

NAN