Home Labarai Zan yi abinda za a riƙa tunawa da marigayiya Asma’u — Gwamna Abba Kabir Yusuf

Zan yi abinda za a riƙa tunawa da marigayiya Asma’u — Gwamna Abba Kabir Yusuf

0
Zan yi abinda za a riƙa tunawa da marigayiya Asma’u — Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin cewa zai yi wani gini da za a riƙa tunawa da marigayiya Asma’u Sani, wacce ta rasu bayan da ya dauki nauyin yi mata aikin tiyata a kasar Indiya amma ta rasu kafin a tashi zuwa Indiya din.

Gwamnan ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da shi da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam, suka kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayiyar a unguwar Alkalawa da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar.

Gwamna Abba ya ce ya yi matukar kaɗuwa da rasuwar yarinyar Asma’u, ya kuma bayyana rasuwar ta a matsayin abin bakin ciki da ban tausayi.

Daga nan sai ya umurci Limamin yankin da ya samo fili domin a gina asibiti ko makarantar Islamiyya, wanda za a sanyawa sunan marigayiya Asma’u.

Sannan kuma ya bayar da umarnin a yi amfani da kudin da aka ware domin kula da marigayiyar wajen daukar nauyin iyayenta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Umrah.

Mahaifin marigayiyar, Malam Sani, wanda ya fashe da kuka bisa karramawar da gwamnan ya yi wa iyalan, ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya tabbatar masa da nasarar zabensa a kotun koli.