30.1 C
Abuja
Friday, June 2, 2023

Ba zan biya wani bashi da Ganduje ya ci bayan zaɓen 18 ga Maris ba — Zaɓaɓɓen gwamnan Kano

Must read

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shawarci hukumomi na gida da na waje da kada su baiwa gwamnatin Ganduje mai barin gado bashi ba tare da yardar shi zaɓaɓɓen gwamnan ba.

Abba Yusuf, a wata sanarwa da kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a yau Asabar ya ce duk hukuma ko ma’aikatar da ta baiwa gwamnatin Kano mai barin gado bashi daga ranar 18 ga watan Maris to ta ɗauki asara domin gwamnatin shi, idan an rantsar da ita, ba za ta biya bashin ba.

A tuna cewa a ranar Alhamis, zaɓaɓɓen gwamnan ya baiwa masu gine-gine a filayen gwamnati shawarar da su dakata.

More articles

Latest article

X whatsapp