Home Labarai Ba zan iya biyan mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70 ba – Gwamnan Gombe

Ba zan iya biyan mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70 ba – Gwamnan Gombe

0
Ba zan iya biyan mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70 ba – Gwamnan Gombe

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya ya bayyana cewa duba da kason da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya, abu ne mai matukar wuya su iya biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 70.

Shugaban kasa Bola Tinubu ne dai ya sanya hannu kan dokar mafi karancin albashin bayan cimma matsaya da kungiyar kwadago.

Da yake jawabi a ranar Talata yayin ganawa da masu ruwa da tsaki kan shirin fara zanga-zanga a fadar gwamnatin jihar, Inuwa Yahya ya ce “Ba zan iya biyan mafi karancin albashi ba kuma ina tsammanin jihohi da dama ma haka abin yake”.

Game da tallafin shinkafa daga gwamnatin tarayya kuwa, Gwamnan ya yaba da tallafin sai dai ya ce har yanzu jihar bata karbi kayan ba.

Da yake jawabi kan shirin zanga zangar kuwa, Gwamnan na Gombe ya bayyana muhimmancin zaman lafiya ga ci gaban jihar.

Sannan ya yi kiran a tattauna a hada kai don magance matsalolin da suka addabi kasar nan.