Gwamnan jihar Kaduna Nasiru el-Rufai rike da dansa Abubakar Sadiq

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai ya bayyana cewar, zai sanya ɗansa mai shekaru 4 Abubakar Sadiq a makarantar Gwamnati da zarar ya cika Shekaru 6 da haihuwa.

Gwamnan Nasiru el-Rufai ya bayyana hakan ne, ranar Lahadi a shafinsa na facebook, inda yake cewa:

“Dana Abubakar Sadiq yanzu shekaransa hudu, kuma islamiyya ya ke zuwa. In ya cika shekara shida zan sashi a makarantar Gwamnati domin babu yadda za’ayi ina shugabantar Al’umma, kuma ace wai yarona na wani makaranta daban da inda yaran talakawa suke.”
“Lokacin muna yara, ya’yan Ministan ilimi na Arewa, Alhaji Isa Kaita, ajinmu daya dasu a nan LEA Kawo. Amma yanzu masu kudi sun kwashe yaran su sun kai su makarantun kudi sun bar yaran talakawa a na gwamnati domin makarantun su cigaba da lalacewa. To mu baza muyi hakan ba da yardan Allah.”