
Kungiyar Kwamarawan Arewa, NCMN, ta bayyana goyon bayanta ga zanga-zangar da ake shirya yi a fadin kasar baki daya.
Kungiyar, a cikin wata sanarwa da shugabanta na kasa, Jabir Ibrahim, ya fitar a jiya Laraba, ta bukaci ƴan Najeriya da su fito ƙwansu da kwarkwatar su domin su kwafi ƴancin su.
Ibrahim ya bayyana zanga-zangar da ake shirin yi a matsayin yakin ceto demokradiyyar kasar.
Kungiyar ta ce halin da al’ummar kasar ke ciki ba abu ne da za a amince da shi ba idan aka yi la’akari da yawaitar sace-sacen mutane da ake yi a watanni 12 na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
“Matasa sun zama mazabar da aka yi watsi da su ba tare da basu wata dama ba, lamarin da ya janyo ‘yan fashi, garkuwa da mutane, da sauran munanan dabi’u a yankin, karancin man fetur da hauhawar farashin kayayyaki da kayayyakin masarufi ya ninka sau uku fiye da shekaru hudu da suka wuce.
“Kudin mu ya zama maras kima, miliyoyin ‘yan Najeriya na fuskantar yunwa saboda tashin farashin abinci da karancin abinci, take hakki da suka hada da ‘yancin fadin albarkacin baki da kungiyanci, ya zama abin tattaunawa a wannan rana.
“Mu hada kai domin neman daukar mataki daga shugaban tarayyar Najeriya domin samar da hanyoyin kawo sauyi domin magance matsalolin tattalin arzikin kasar,” in ji ƙungiyar.