
Wasu almajirai dake bara a titunan jihar Kano, sun roƙi masu shirya zanga-zanga da su tausaya wa al’umma su dakata haka.
Baba Haliru mai shekaru 70 daga Rijiyar Zaki, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN cewa suna sha wahalar rayuwa sakamakon zanga-zangar, wacce ta tsayar da harkoki a jihar.
Haliru ya yi bayanin cewa Almajirai da dama sun dogara ne da abinda suke samu a kullum wajen ciyar da iyalansu, inda ya koka da cewa zanga-zangar ta dakatar musu da hanyar samun na sakawa a bakin salati.
Ya koka da cewa, “Ba mu samu mun ci abinci ba tsawon kwanaki a gidajen mu, sai ruwa mu ke sha.
” Don Allah, a faɗawa masu zanga-zanga su kawo karshenta, su tattauna da gwamnati”.
Shima wani Almajirin ya nemi a kawo karshen zanga-zangar da kuma janye dokar hana fita.
Malama Maryam Kabiru da ke unguwar Hotoro ta ce “Abincin mu ya kare kuma babu damar fita don samowa, bamu da kudi, lamarin ya zafafa”.
Shi ma Malam Isa Musa na unguwar Dorayi ya roki gwamnati da ta samar da matakai na tallafawa dattawa wadanda basu da masu tallafa musu.
Ya ce ” Muna bara ne domin bamu da masu tallafa mana. Tun da aka sa dokar hana fita bama samun abinci tsawon kwanaki 3.
“Ba za mu iya ci gaba da zama a haka ba; don haka a dakata da zanga-zanga”.
Sai dai kuma, a ranar Talata ne gwamnatin jihar ta sanar da sassauta dokar hana fita daga karfe 6 na safe zuwa shida na yamma.
Sassauta dokar da gwamnatin ta yi ya sanya harkoki sun fara dawowa yadda su ke a jihar, wacce ta yi shura a kasuwanci, inda hakan zai baiwa almajiran dama ci gaba da samun sadaka don samin daukar nauyin dawainiyar su ta yau da kullum.
NAN