Home Labarai Zanga-zanga: Ka saurari koken ƴan Nijeriya, Ndume ya shawarci Tinubu

Zanga-zanga: Ka saurari koken ƴan Nijeriya, Ndume ya shawarci Tinubu

0
Zanga-zanga: Ka saurari koken ƴan Nijeriya, Ndume ya shawarci Tinubu

Tsohon Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya saurari bukatun ƴan Nijeriya wadanda ke shirin yin zanga-zanga.

Ndume ya yi wannan kiran ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a wani shirin sa mai taken Politics Today.

Da aka tambaye shi ya yi tsokaci kan kiran da shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) Joe Ajaero ya yi wa shugaban kasar na ya tattauna da ƴan kasa, Ndume ya ce ya amince da wannan kira.

Ya ce, “Na yi goyi bayan wannan kira nasa. Shugaban NLC ne ya gabatar da wannan kudiri. Ka ce masa ina goyon bayan kudirinsa na cewa shugaban kasa ya saurari ‘yan Najeriya.

“yau kwanaki 26 daga harin da aka kai a Gwoza. Jama’ata suna ta faman kokarin komawa gona; muna fafutukar tsira. Muna iya ganin gwamnatin jihar da sauran hukumomi suna kokarin taimaka mana. Muna fama da wannan yanayin; ba mu da lokacin yin zanga-zanga.

“Don nuna rashin amincewa da wa? Ina shakkun ko za a gudanar da zanga-zangar a Maiduguri. Wannan ba wai ina hana mutane su yi kokensu ba ne, tsoro na shi ne kallon abin da ya faru yayin zanga-zangar ta EndSARS.

” Ina fatan ba za ta rikice ta zama rigima ba kuma musamman ma lokacin da ba a dan jagorancin ba. Hatta kungiyar kwadagon da suka yi yajin aiki sau da dama, yanzu kawai muna ganin suna ta fama ln kokarin gudanar da zanga-zanga. Amma ban san su waye jagororin ba.”