Home Labarai Zanga-zanga: Wata ƙungiya ta ɓullo don samar da mafita a Arewa, ta naɗa Shekarau jagora

Zanga-zanga: Wata ƙungiya ta ɓullo don samar da mafita a Arewa, ta naɗa Shekarau jagora

0
Zanga-zanga: Wata ƙungiya ta ɓullo don samar da mafita a Arewa, ta naɗa Shekarau jagora

Wata sabuwar ƙungiya ta wasu gogaggun ƴan siyasa a arewacin Najeriya, ta ce ta fara lissafin samar da mafita ga yankin.

Wasu da suka kira kansu masu kishin arewacin Najeriya sun ɓullo da sabon yunƙurin ne da nufin sama wa yankin ingantaccen shugabanci da alkibla ta fuskar siyasa da tattalin arziki da zamantakewa.

Sun kira wannan yunƙuri nasu da taken ”League of Northern Democrats”, a turance – wani taron dangi na wasu masu fada a ji na areawacin Najeriya, da suka hada da tsofaffin gwamnoni da ma’aikatan gwamnati da ‘yansiyasa da tsofaffin sojoji da ‘yan sanda, da sauran masu ruwa da tsaki na yankin.

BBC Hausa ta rawaito cewa a taron da suka gudanar a Abuja a jiya Talata, sun amince da naɗa tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau a matsayin jagora.

Mahalarta taron sun ce sun yi la’akari da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a ƙasar wadda ta ƙara nuna wa duniya irin girman ƙalubalen da yankin arewa ke fuskanta.

“Yunwa da talauci da jahilci ne suka addabi yankin arewa,” a cewar ɗaya daga cikin mahalarta taron, Danburan Zazzau, Muhammad Sani Sha’aban, wani ɗansiyasa daga jihar Kaduna.

Shugaban tafiyar, Malam Ibrahim Shekarau ya ce, matsalolin arewa sai kara haɓaka suke, don haka dole a zauna a nemi mafita.

“Ana ta surutun cewa arewa ta lalace, matasa sun lalace, ba shugabannin kirki, ana ta sace kudaden mutane, shi ya sa muka tsinto masana, gogaggu a fannoni daban-daban mu kusan 200,”

“Babbar manufarsu ita ce, waɗanne matakai za mu ɗauka na faɗakar da al’ummar arewa game da mutanen da ya kamata su shugabance su,” in ji Shekarau.