Home Labarai Zanga-zanga: Daƙyar ƴan Nijeriya ke cin abinci sau ɗaya a rana, ya kamata shugaban ƙasa ya tashi tsaye — NLC

Zanga-zanga: Daƙyar ƴan Nijeriya ke cin abinci sau ɗaya a rana, ya kamata shugaban ƙasa ya tashi tsaye — NLC

0
Zanga-zanga: Daƙyar ƴan Nijeriya ke cin abinci sau ɗaya a rana, ya kamata shugaban ƙasa ya tashi tsaye — NLC

Shugabannin kungiyoyin kwadago na kasa, sun shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakile zanga-zangar da ta kunno kai a fadin kasar ta hanyar tattaunawa da wadanda su ke shirya ta.

Daily Trust ta rawaito cewa daruruwan ‘yan Najeriya na gangami domin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar .

Da ya ke tsokaci kan lamarin, shugaban kungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya bukaci shugaban kasar da ya gano jagororin zanga-zangar ya tattaunawa da su.

Ajaero ya kuma yi kira ga Tinubu da ya saurari kukan jama’a, inda ya kara da cewa miliyoyin ‘yan Najeriya ba sa jin dadin halin kuncin da kasar ke ciki.

Shugaban ƙwadagon ya lura da takaicin cewa matsin tattalin arzikin ƙasar ya sanya iyalai da yawa ba sa iya cin abinci sau ɗaya a rana.