Home Labarai Zanga-zanga: Zaman lafiya ya fara dawo wa a Kano bayan sassauta dokar hana fita

Zanga-zanga: Zaman lafiya ya fara dawo wa a Kano bayan sassauta dokar hana fita

0
Zanga-zanga: Zaman lafiya ya fara dawo wa a Kano bayan sassauta dokar hana fita

Daga Salisu Ali

Al’amura sun fara komawa yadda su ke a fadin jihar Kano bayan zanga-zangar adawa da matsin tattalin arziki da aka fara ranar 1 ga watan Agusta.

DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito cewa zanga-zangar dai ta rikiɗe zuwa rikici, wanda ya kai ga lalata kadarorin gwamnati da na al’umma tun a ranar farko.

Daga cikin kadarorin da bata gari suka lalata da sunan zanga zangar sun hada da cibiyar hukumar NCC dake titin gidan Gwamnatin jihar Kano wacce aka tsara budewa a cikin watan nan na Agusta.

Bayan samun ɓarnar ne dai gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fita ta tsawon awanni 24 a fadin jihar.

Sai dai kuma duk da dokar hana fitar, an samu wasu da suka fito zanga-zangar, musamman a ranakun Juma’a da Asabar da Lahadi, har rahotanni su ka tabbatar da samun asarar rayuka a unguwar Kurna da Bachirawa yayin arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro.

Sai dai al’amura sun fara daidaita a jihar ta Kano a yau Laraba bayan gwamnatin jihar ta sassauta dokar daga 6 na safe zuwa 6 na yamma.

Binciken da DAILY NIGERIAN HAUSA ta yi ya nuna an bude kusan dukkan manyan kasuwannin jihar, inda al’umma su ka fara koma wa harkokinsu na yau da kullum.

Manyan kasuwanni irinsu: Dawanau da Kantin Kwari da Sabon Gari da Kofar Wambai da Singer duk sun kasance a bude, sai dai kuma wakilin mu ya gano cewa akwai tsaro a bakin kasuwannin.

Hakazalika, an hangi jami’an tsaro na gadin wasu daga cikin manyan makarantun, inda bankuna da gidajen mai sun kasance a bude a daidai lokacin da babu wata alama ta fitowar masu zanga-zanga.

Sai dai, an samu karin farashin mai a wasu gidajen man na jihar Kano, inda ake siyar da duk lita daya kan Naira 950 maimakon farashin Naira 800 da aka siyar a kwanakin baya.

A zantawar da Jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA ta yi da wasu mazauna Kano, suma sun bayyana damuwa kan yadda aka samu karin farashin kayan abinci a kasuwar Singa dake Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu karin kusan Naira dubu 20 a buhun Fulawa da karin dubu 4 a Taliya wacce a baya ake siyarwa kan Naira dubu 14 ta koma 18.

Sai dai tuni rahotanni suka bayyana cewa, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gayyaci shugabannin ‘yan kasuwa domin zaman gaggawa kan lamarin.

Bayan lafawar al’amura dai a jihar, al’umma na fatan Gwamnati za ta kara sassauta dokar takaita zirga zirgar.