
Mambobi huɗu na Kwamitin Koli na Kasa, NWC, na jam’iyyar adawa ta PDP, sun mayar da kuɗi naira miliyan 122.4 da shugabannin jam’iyyar suka saka musu a asusunsu.
Sun mayar da maƙudan kuɗaɗen ne a daidai lokacin da ake zargin shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, da laifin bai wa mambobin NWC ɗin cin hanci domin rufe bakinsu kan badaƙalar sama da Naira biliyan 10 da yayi ta kuɗaɗen foma-fomai da aka siyar wa ƴan takara.
Mambobin kwamitin da suka mayar da kudaden sun hada da mataimakin shugaban jam’iyya na Kudu maso Yamma, Olasoji Adagunodo; mataimakin shugaban jamiyya na Kudu, Taofeek Arapaja; mataimakin shugaban jam’iyya na Kudu, Dan Orbih da; shugabar mata ta kasa, Stella Affah-Attoe.
DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa, Mista Arapaja ya samu Naira miliyan 36, yayin da Orbih, Effah-Attoe da Adagunodo suka samu Naira miliyan 28.8 kowanne.
Amma a cikin wasiƙu daban-daban da aka aika wa shugaban jam’iyyar, mai kwanan wata 29 ga Satumba 2022, manyan jami’an jam’iyyar sun sanar da shugaban matakin da suka yanke na mayar da kuɗin bayan ” rahotannin kafofin watsa labaru marasa daɗi “.