30.1 C
Abuja
Friday, June 2, 2023

Zargin cin zarafi: Kotu ta tura tsohon ɗan wasan Barcelona, Dani Alves gidan yari

Must read

Wata kotu a ƙasar Sifaniya ta bayar da umarnin tsare ɗan wasan Brazil Dani Alves a gidan yari har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci a kan shari’ar da ake yi masa kan zargin cin zarafin wata mata.

A ranar Juma’a ne aka tsare ɗan wasan mai shekara 39 a birnin Barcelona.

Alves wanda tsohon ɗan wasan Barcelona ne ya musanta zargin cewa ya ci zarafin wata mata a wani gidan rawa.

Kan wannan batun dai tuni ƙungiyar da ɗan wasan ke taka wa leda Pumas UNAM ta ƙasar Mexico, ta ce ta soke kwantiragin ɗan wasan nan take.

More articles

Latest article

X whatsapp