
Malamin addinin Musulunci na Jihar imamin Kano, Abduljabar Nasiru Kabara, a jiya Alhamis ya zargi lauyansa, Dalhatu Shehu Usman, da laifin karɓar Naira miliyan 2 domin bai wa alkalin babbar kotun Shari’a ta Kano cin hanci a cigaba da shari’arsa.
NAN ya ruwaito cewa ana tuhumar Abduljabbar ne da laifuka guda hudu da suka shafi kalaman batanci ga Annabi Muhammad, Tsira da aminci su tabbata a gare shi.
A ci gaba da zaman shari’ar da ya gudana a kotun a jiya Alhamis, Lauyan wanda da ake kara, Dalhatu ShehuUsman, wanda Muhammad Lawan ya wakilta, a cikin rokonsa, ya buƙaci kotun da ta ƙyale wanda ake kara ya gabatar da rubutaccen bayaninsa na ƙarshe da kansa.
Wanda ake karar, yayin da yake gabatar da rubutaccen bayaninsa, mai kwanan wata 20 ga watan Satumba, ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar da gwamnatin jihar Kano ta shigar a kansa tare da umurtar gwamnatin jihar da ta ba shi hakuri.
“Ina kira ga kotu da ta dauki rubutattun bayanai a matsayin hujjata kan wannan shari’a a matsayin shaida da kuma wa’azi na na sauti.
“Lauyana ya zo gidan yarin ya shaida min cewa alkali ya umarce shi da ya karɓi Naira miliyan 2 domin ya sallame ni.
“Lauya na ya ce min ya ba alkali Naira miliyan 1.3, wani mutum kuma Naira 200,000, shi kuma da kansa ya ɗauki Naira 500,000,” inji shi.
Lauyan masu gabatar da kara, Mamman Lawan Yusufari, SAN, a cikin rubutaccen bayaninsa na karshe, mai kwanan wata da kuma kammala wa 22 ga watan Satumba, ya bukaci kotu ta yanke wa wanda ake kara hukunci bisa ga doka tare da daukar bayanansu a matsayin shaida a kan wanda ake kara.
Masu gabatar da kara sun rufe karar nasu ne da shaidu hudu da za su tabbatar da shari’ar, yayin da wanda ake tuhuma ya gabatar da shaida guda daya da litattafai 24 da kuma katin ma’adanar sauti, wato memory card da ke tabbatar da kararsa.
Alkalin kotun, Ibrahim Sarki-Yola, ya musanta zargin karbar cin hanci.
Ya ce daga baya za a sanar da ranar yanke hukunci ga bangarorin biyu.
Ana zargin wanda ake tuhumar da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad, SAW, a aurensa da Nana Safiyya a Jautul Fara, sashe na 93 (40) da hadisi na 1,365 da 1,428. Sahih-Bukhari da Muslim.
Da yake magana da manema labarai bayan zaman kotun, Shehu-Usman ya musanta zargin karbar cin hanci.
“Ban yi mamaki ba. Wanda na ke karewa ya kuma yi wasu zarge-zarge a kan sauran lauyoyinsa guda uku a baya,” in ji Mista Shehu-Usman.