Home Lafiya Zazzaɓin Lassa ya hallaka mutane 80 a Nijeriya, in ji NCDC

Zazzaɓin Lassa ya hallaka mutane 80 a Nijeriya, in ji NCDC

0
Zazzaɓin Lassa ya hallaka mutane 80 a Nijeriya, in ji NCDC

 

Cibiyar Daƙile Cututtuka ta Ƙasa, NCDC, ta ce mutane 80 ne su ka rasu da ga annibar cutar zazzaɓin lassa da ga ranar Alhamis.

NCDC ya baiyana haka ne a yayin jawabin ta na bayanan yayayin Zazzaɓin Lassa na ƙasa a Abuja.

Rahoton na NCDC ya baiyana cewa an samu ɓullar cutar har guda 434 a faɗin ƙasar nan.

Rahoton ya zaiyano jihohin da a ka samu ɓullar cutar da su ka haɗa da 190 a Jihar Edo, 150 a Ondo, 21 a Taraba, 17 a Ebonyi, 15 a Bauchi, 8 a Benuwe.

Rahoton ya ƙara da cewa an samu ɓullar cutar a kan mutane 8 a Filato sai kuma a ka samu 7 Kaduna a Kaduna.

Sai kuma Jihar Enugu 5, Nasarawa 3, Kogi 3, Kross Riba 1, Imo 1, Anambra 1, Delta 1, Abia ma guda 1.

Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa NCDC ta shawarci ƴan ƙasa da cewa duk wanda ya ji alamun Zazzaɓin Lassa ya yi maza ya kira layikan kar-ta-kwana da Hukumar Lafiya ta Ƙasa ta bayar ko lambar 6232.

Alamomin Zazzaɓin Lassa sun haɗa da ciwon kai, ciwon jiki da kasala ko kuma fitar jini ta baki ko hanci.