29.1 C
Abuja
Friday, January 28, 2022

Zulum ya nemi da a kyautata albashi da walwalar sojojin Nijeriya

Must read

 

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya yi kira da a kyautata albashi da walwalar sojojin Nijeriya, domin a ƙara musu ƙara musu karsashi wajen kare ƙasar nan.
Zulum ya yi kiran a yayin taron taya Babban Kwamandan Rundunar Soji ta mai riƙon ƙwarya, Abdulwahab Eyitayo,  murnar ƙarin girma zuwa Manjo Janar a jiya Lahadi a Maiduguri.
Zulum ya nuna cewa sojin Nijeriya sun sadaukar da ran su, kuma wasu har sun rasa rayukan su waje kare Nijeriya, in da ya ƙara da cewa ya kamata a saka musu a bisa wannan sadaukarwar ta su.
Ya kuma taya Eyitayo murna da sauran ofisoshin da a ka ƙarawa girma, inda ya ce jihar Borno da al’ummar ta na taya su murna.
Gwamnan ya baiyana ƙudurin gwamnatin sa wajen tallafawa sojoji domin samun nasarar yaƙi da ta’addanci.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article