
Daga Ashafa Murnai Barkiya
1. Gamna Ganduje ya zubar da mutuncin Shugaba Muhammadu Buhari. Duk da kururuwar da Gwamnatin APC ke yi cewa za a samu canjin tafiyar siyasar kasar nan, hakan ya nuna ba gaskiya ba ne.
2. Gwamna Ganduje bai dauki Fadar Shugaban Kasa da daraja ba, domin ta kira shi, kuma ta kira Kwankwaso domin a samu zaman lafiya a Kano. Gwajin Makaman da Ganduje ya yi, ya tabbatar da gaskiyar zargin da Kwankwaso ya yi cewa an yi shirin afka musu idan sun kai ziyara a Kano.
3. Kimar Kwamishinan ‘Yansandan Kano ta ragu sosai a idon jama’a, idan ma ba ta zube ba. Wanda ya nemi hana Kwankwaso taro, sai ga shi gwamnatin jihar ta shirya ‘gwajin makamai’ a gaban sa. Ni ma na goyi bayan cewa ba adali ba ne, a dauke shi daga Kano.
4. Sufeto Janar na ‘Yansanda ya kyale Kwankwaso ya yi na shi taron, tunda dai har Ganduje ya yi na shi bajekolin, kuma a ranar da ya kamata Kwankwaso ya yi taron sa.
5. Jam’iyyar APC ta ba talakawa kunya da har ta daure wa Ganduje gindin gudanar da irin wannan mahaukacin taro. Duk wanda ya tuna alkawurran da ku ka yi wa jama’a na gyara kasar nan, ya san cewa kun yi ta aibata PDP ku na nuna hotunan magoya bayan su dauke da makamai, ku na cewa za ku canja.
6. Duk wanda ya dauko mana irin wannan haukan ya nemi ya saka mana shi a cikin ajandojin sa na 2019, to mu ma za mu ci gaba da yakar sa a kafafen sadarwa, ko wane ne shi, za mu ci gaba da nuna wa jama’a illar sake zaben sa.
7. Yanzu kuma da wane bakin magana magoya bayan APC za su ci gaba da aibata wasu? Canjin da mu ka yi ta fafutikar kawowa a 2015 kenan?
8. Akwai babbar matsala ga Shugaba Buhari a kamfen din 2019, tunda har ya yi likimon da ya bari ‘yan-takifen siyasa su ka shiga gaban sa, su ka canja wa APC sabon launin tambarin jam’iyya, su ka maye gurbin wanda aka sani da takubba, sanduna, adduna, gariyo, barandami da duk wani makamin tayar da hankulan jama’ar da aka yi wa romon-kunne a 2014, aka ce za a samu canji.
9. Shekara uku cur mu ka yi, mu na rubuce-rubucen kawo canji. Amma wasu ‘yan takife na neman maida wahalar da mu ka yi ta zama wahalar banza. Sun kimshe na su ‘ya’yan a gida da cikin manyan makarantu, sun bar talakawa dauke da takubba da barandami.
Wannan ra’ayi na ne, amma duk wanda ya tsargu, to da shi na ke!