
Fitaccen attajirin nan kuma Shugaban kamfanin Forte Oil, Femi Otedola ya amsa bukatar jam’iyyar PDP na yi mata takarar Gwamnan jihar Legas a zaben 2019 dake tafe.
Otedola zai yi takara da Akinwunni Ambode Gwamnan jihar Legas na yanzu kuma mai neman wa’adin mulki na biyu a jam’iyyar APC.
Fitaccen dan Jarida Dele Momodu je ya bayyana labarin inda yace Otedola ya tabbatar masa da cewar ya amsa bukatar ta PDP domin yi mata takarar Gwamnan Legas.