
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta shawarci kafafen yada labarai da su yi taka tsantsan akan irin rahotannin da zasu dinga yadawa dangane da babban zaben 2019 da yake tafe.
Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu, ne ya bayyana haka a wani taro na kungiyar editoci ta kasa wadda ofishin jakadancin Amurka dake birnin Legas a Najeriya ya shirya.
Farfesa Yakubu, wanda babban baturen zabe na jihar Legas Olumekun Sam ya wakilta, wannanbatu yana da matukar hadari yada bayanan da ba na gaskiya ba akan zabubbukan dake tafe, “Tilas duk labarin da za’a bayar ya zama sahihi ne daga hukumar zabe ta kasa ko wakilanta dake jihohi”
Yace idan aka yi la’akari da zabubbukan da suka gabata a baya, kafafen yada labarai sun taka muhimmiyar rawa kwarai da gaske wajen samun sahihin sakamako ko akasinsa.
“Wasu daga cikin masu bayar da rahotannin zabubbuka basa gudanar da sahihancin labarin da suka samu, sabida azarbabi suke yada shi”
Ya kara da cewar, a sabida irin muhimmanci da kuma irin gudunmawar da kafafen yada labarai suke bayarwa, muke fatan zasu yi amfani da gogewa da kuma basira wajen isarda labaran zabe ga al’umma.
Haka kuma babban bako mai jawabi a yayin taron Mista Momoh wanda shi ne Shugaban gidan Radiyon Muryar Najeriya, yayi gargadi akan sabbin shafukan yada labarai da ke kan sabbin kafafen sadarda zumunta dake kan Intanet, irin yadda suke sharara karya ba tare da bincike ba.
Manyan masana da yawa sun tofa albarkacin bakinsu kan batun inda suka yi gargadi kan yada labaran da ba sahihai ba, da ka iya jawo cecekuce.