
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar Shugabancin Najeriya a zaben 2019 dake tafe a shekara mai zuwa, a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
Shekarau wanda tsohon Ministan Ilimi ne, ya bayyana a wata wasika da ya aike mana, inda yake bayyana mana aniyarsa ta neman kujerar Shugabancin Najeriya idan jam’iyyarsa ta PDP ta bashi damar zama dan takararta.
Kamar yadda ya bayyana a wasikar da ya aike mana “Ina fatan kuna sane da cewar, tun bayan zaben 2015 da ya gabata, akwai kiraye kiraye daga mutane da dama ciki da wajen kasarnan, inda suke bukatar na tsaya takarar Shugabancin Najeriya a zaben da ke tafe na 2019, domin ceto halin da al’ummar kasarnan suke ciki”
“Na san mutane da yawa suna wannan kiran na tsayawa ta takarar Shugaban kasa ne, saboda yarda da amincewa da suka yi da ni, da kuma burin da suke da shi na ganin ni zan iya cire musu suhe daga wuta”
“A saboda haka ne, na zagaya dukkan sassan kasarnan guda shida, inda na zauna da mutane da abokai domin neman shawarwari da kuma nazartar halin da za’a tunkara idan halin fitowar yayi”
“Bayan wannan zagaye da neman shawarwari da na yi a dukkan fadin Najeriya, na gamsu da kiraye kirayen mutane, na kuma aminta cewar abinda ake fatan na yi zan iya yinsa, don haka ne na amsa kiran da al’ummar Najeriya suke yi min na fitowa takarar Shugaban kasa a zaben 2019 dake tafe” A cewar Malam Ibrahim Shekarau
Dailytrust.com