Home Labarai 2019: Sanata Dino Melaye yace APC ta mutu

2019: Sanata Dino Melaye yace APC ta mutu

0
2019: Sanata Dino Melaye yace APC ta mutu

Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Dino Melaye ya bayyana cewar jam’iyyar mai mulki ta APC tana tunkarar dukkan hanyoyin faduwa a zaben 2019 idan har irin rikita rikitarda jam’iyyar take fama da ita ta cigaba.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar Sanata Melaye, wanda yake fama da matsaloli da yawa, ko a makon da ya gabata rundunar’yan sanda ta kasa reshen jihar Kogi ta bayyana cewar tana nemansa ruwa a jallo, saboda zarginsa da taimakawa kungiyoyin ‘yan daba.

Bayan haka kuma,kotun daukaka kara  ta baiwa hukumar zabe damar cigaba da yiwa Sanatan kiranye daga zaman dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Kogi ta yamma a majalisardattawan Najeriya.

Akwai tsattsamar alaka tsakanin Gwamnan jihar Kogi Yahya Bello da shi Sanata Dino Melaye da kuma bambanci mai yawa tsakaninsu.

A lokacin da yake magana da sashin Hausa na BBC wanda DAILY NIGERIAN ta bibiya, Mista Melaye yayi kukan cewar jam’iyyar ta sa na cikin tsaka mai wuya, domin a cewarsa, masu rike da mukamai a cikin jam’iyyar kowanne na kwashe kafar dan uwansa.

“Akwai rikita rikita a cikin jam’iyyar APC da yawa, ya zama dole a fadi gaskiya kan hakan. Kowa na cin dunduniyar dan uwansa, ko dai a tsaya a sasanta wannan rikici ko kuma jam’iyyar ta kai kanta makabartar tarihi a zaben 2019”

Melaye ya bayyana cewar gwamnan jihar Kogi Yahya Bello yana ta shirya masa makarkashiyar ganin ya ga bayansa, da kuma sanyawa a kashe shi.

Ya kuma bayyana cewar duk wannan gwagwarmayarda yke yi yana yi ne domin talakawa da kuma cigabansu da fatan ganin sun sami kyautatuwar rayuwa.