Home Nishaɗi Boyayyen labarin Jaruma Sadiya Idris da ya kamata ku sani

Boyayyen labarin Jaruma Sadiya Idris da ya kamata ku sani

0
Boyayyen labarin Jaruma Sadiya Idris da ya kamata ku sani

Daga Hassan Y.A. Malik

Sadiya Adam Idris na daya daga cikin jaruman Kannywood mata da suka sha fama da daraktoci da furodusoshi kan sai ta yi soyoayya da su sakamakon kyan diri da kyawawan idanu da Ubangiji ya yi wa jarumar.

Wannan dalili ne ma ya sanya furodusoshi suka yi ta rige-rigen sanya ta a manyan finafinai kuma suka yi ta biyanta manya kudade sama da tsararrakinta don su samu kanta, dalilin da ya sanya cikin dan kankanin lokaci ta yi shuhura.

Sai dai wani abinda mutane basu sani ba game da Sadiya Adam shi ne, Sadiya yarinya ce mai rikon addini, domin ma kuwa bincike ya nuna cewa tana daya daga cikin kalilan na mata jarumai da za su iya kawo Baqara zuwa Nasi.

A lokacin da  Sadiya ta zo Kano shekaru 4 da suka gabata, ta hadu da wani matasshin dan kasuwa mai suna Sanusi Ahmad, wanda da ne a wajen Ciroman Kantin Kwari kuma mai unguwar Rijiya Biyu a cikin kwaryyar birnin Kano.

Sanusin ne ma ya kamawa Sadiya gida kuma ya kawata mata shi yadda ta ke bukata, kana kuma ya saya mata tsadaddiyar mota.

Wannan ya sanya abokan aikinta suka fara kyashinta sakamakon karbuwa da kuma babbar yarinya da ta zama cikin dan karamin loto.

Sai dai daukaka da kuma dukiyar da Sadiya ta samu sam bai dadata da kasa ba, hasali ma dai, sai ya kasance jarumar ta ci gaba da bayyana burin da ya kawo ta Kano na ta zama fitacciyar jaruma bayan nan kuma ta samu miji ta yi aure ta zauna a gidanta har abada.

Allah kuwa ya amshi addu’ar Sadiya domin kuwa ya bata duk abinda ta roka a zuwanta Kano. Ita da Sanusi suka shirya angwacewa a ranar 17 ga watan Nuwamban, 2017, amma kash! Sai shirin nasu ya gamu da tasgaru sakamakon son jarumi Ramadan Booth da ya kamata da har ya sanya ta nemi ta fasa auren Sanusi.

Ko da matsin lamba ya yi wa Sadiya yawa na cewa Ramadan fa ba aurenta zai yi ba sai ta saduda ta sake sanya ranar aurenta a matsayin ranar 1 ga watan Afrilu, 2018.

Nan ma dai sai aka sake samun matsala sakamakon kin amincewa da iyayen Sanusi suka yi na ya auri ‘Yar Fim’, kamar dai yadda majiyarmu ta bayyana mana.

Daga bangaren iyayen Sadiya ma dai an samu irin waccan matsalar sakamakon wai su sun fi amincewa da Sadiya ta koma gida Maiduguri ta auri dan uwanta.
Hakan ya sanya dole Sadiya ta tattara ya-nata-ya nata ta koma Maiduguri kuma ta daina ko yin waya da abokan aikinta na Kannywood.

Can daga baya kuma sai jita-jita ta ci gaba da yaduwa a industiri na cewa fa batun auren Sadiya a ranar 1 ga watan Afrilu, 2018 na nan ba a fasa ba sakamakon ganin kawayenta na kusa suna ‘yan shirye-shirye.

An dai daura auren a garin Kano a ma masallacin Umar Bin Khattab da ke shataletalen Dangi, inda kashegari amarya ta gayyaci kawayenta zuwa wani kasaitaccen walima a Magajin Rumfa da ke unguwar Nassarawa Kano, walimar da ta samu halartar tsofaffi da jarumai mata na wannan zamani.

wasegari dai har lau, Sadiya ta sake shirya wani bikin al’adarsu ta barebari da suke kira da ‘Wushe-wushe’, kuma shi ma ya samu halartar ‘yan uwa da abokan arziki da dama daga ciki da wajen Kannywood., kuma an ci an sha daga abincin gargajiyar barebari.

Bayan an kai Sadiya dakinta ne sai ta rubuta a shafinta na Instagram cewa tana bukatar ‘yan uwa da abokan arzuka da su taya ta da addu’ar samun zaman lafiya a gidan mijinta.

Sai dai wata majiya ta ce wasu daraktoci da furodusoshin Kannywood basa yi wa Sadiya fatan ta zauna a gidan mijin nata, saboda basu koshi da samun riba daga irin rawar da jarumar ke takawa a finafinai ba, a cewar majiyar.