
Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, NIS, ta tabbatar da kamun da aka yiwa Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta Yamma a majalisar dattawan najeriya, Dino Melaye, a filin sauka da tashin jiragen saman kasa da kasa dake babban birnin tarayya Abuja a safiyar Litinin.
Kakakin hukumar, Sunday James, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, cewar jami’an hukumar NIS ne suka kama Sanata Melaye kamar yadda aka basu umarni su kama shi.
Hukumar sun tabbatar da kame Sanata Melaye ne, awanni bayan da Sanatan ya wallafa a shafinsa na Twitter da misalin karfe 7:32 na safe,inda yace an kama shi.
“Yanzun nan aka kama ni a masaukin alfarma na filin jiragen sama na Namdi Azikiwe dake Abuja akan hanyata ta zuwa kasar Maroko, bisa wani aiki da Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tura ni can kasar” Abinda Melaye ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A kwanakin baya ne dai, runudnar ‘yan sanda ta kasa ta bayyana sunan Dino Melaye a matsayin wanda take nema ruwa a jallo, saboda zargin da ake yi masa na shigo da wasu makamai zuwa ga wasu ‘yan ta’adda da suka ce shi ne ya shigo musu da makaman.
Sai dai kuma, tuni Sanata Melaye ya nesanta kansa da wancan zargi da aka yi masa na shigo da makamai, inda ya bayyana abinda da cewar siyasa ce tsagwaronta don a bata masa suna.
NAN