
Wasu gungun ƴan daba, ɗauke da muggan makamai ne su ka ƙona ofishin kamfe na ƴan ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau a jam’iyar APC.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa ɗaruruwan ƴan daban sun dira a ofishin da ke Titin Maiduguri, a birnin Kano, inda su ka faffasa kujeru da tebura, gami da allukan da ke ɗauke da fastocin ƴan takara, sannan su ka ƙone wani sashe na ofishin.
A jiya Laraba ne dai gwamnatin Kano ta garƙame ofishin lauyan da ya tsayawa ɓangaren Shekarau, Nureini Jimoh, su ka samu nasara a shari’ar da kotu ta rushe shugabannin jam’iya na Kano, ƙarƙashin Abdullahi Abbas.
Ƙarin bayani na nan tafe…