
Rundunar Ƴan Sanda ta Ƙasa ta tsawaita wa’adin yin rijistar neman aikin ta yanar gizo ga ƴan ƙasa masu sha’awar yin aiki a hukumar.
A sanarwar da Kakakin rundunar na ƙasa, Frank Mba ya fitar a yau Juma’a, rundunar ta ce sabon wa’adin rufe yin rijistar ya koma 22 ga watan Janairu 2022.
A cewar sa, ƙarin wa’adin ya faru ne sakamakon bukatar manema aikin da ga Kudu-maso-Gabas da kudu-maso-kudu su cike kason yankunan su.
“Shafin na aika neman aikin zai ci gaba da zama a buɗe har sai tsakar daren sabon wa’adin da a ka ƙara.
“Sannan an kara wa’adin ne domin a tabbatar an yi rabon kason aikin daidai, musamman a yankunan Kudu-maso-Gabas da Kudu-maso-Kudu da kuma Jihar Legas domin a basu damar su cike kason su.
“Ƙididdiga ta nuna cewa mutane 81,005 su ka aika neman aikin a fadin ƙasar nan da ga 7 ga watan Janairu. Daga cikin wannan adadin, 1,404 ne kawai, daidai da kashi biyu, su ka fito daga yankin Kudu-maso-Gabas, 261 da ga Legas, sai jihar Anambra mai adadi mafi karanci shine 158.
“Mu na baiwa masu aika neman aikin shawarar da su kira 08100004507 domin tambaya idan har su na fuskantar wata matsala wajen aikawa,” in ji Mba.
Rundunar ta jaddada cewa aika neman aikin kyauta ne.