Home Labarai NBC ta karɓe lasisin gidan talabijin na AIT, Silverbird da sauran kafofin watsa labarai 50

NBC ta karɓe lasisin gidan talabijin na AIT, Silverbird da sauran kafofin watsa labarai 50

0
NBC ta karɓe lasisin gidan talabijin na AIT, Silverbird da sauran kafofin watsa labarai 50

 

Hukumar kula da tashohin Watsa Labarai ta Kasa, NBC, ta kwace lasisin gidan rediyo da talabijin na AIT/Ray Power FM, da ke ƙarƙashin kamfanin DAAR Communication L.td., Silverbird TV Network da wasu gidajen rediyo da talabijin 50 kan bashin Naira biliyan 2.6 da a ke bin su.

Babban Daraktan NBC, Balarabe Ilelah, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a yau Juma’a a Abuja, ya ba da umarnin rufe tashoshin da abin ya shafa nan da sa’o’i 24 masu zuwa.

Ilelah ya umurci ofisoshin NBC a duk faɗin kasar nan da su haɗa kai da jami’an tsaro don tabbatar da biyayya ga umarnin cikin gaggawa.

Ya bayyana cewa a watan Mayun 2022, hukumar ta buga a cikin jaridun kasar nan, jerin sunayen masu lasisin da BBC ke bin bashi, inda har ta ba su wa’adin makonni biyu su sabunta lasisin su da biyan basussukan da ake bin su, ko kuma su rasa lasisin su tare da cire masu na’urorin watsa shirye-shirye.

“Bayan an buga sanarwar, wata uku wasu masu lasisin har yanzu ba su biya basussukan da ake bin su ba, wanda ya saɓawa dokar NBC Act CAP N11, na dokokin tarayyar Najeriya ta shekarar 2004, musamman sashe na 10 (a) na jaddawali na uku na dokar.

“Saboda wannan ci gaba, ci gaba da gudanar da ayyukan tashoshin da a ke bi basussuka ya sabawa doka kuma yana zama barazana ga tsaron ƙasa.

“Saboda haka, bayan nazari mai zurfi, hukumar NBC ta sanar da soke lasisin waɗannan tashoshin tare da ba su sa’o’i 24 su rufe ayyukansu,” inji shi.